Tuesday, November 5, 2024
More
    HomeLabaraiManoma sun koka kan sakaci da wuraren noman rani a Daura

    Manoma sun koka kan sakaci da wuraren noman rani a Daura

    Dubban manoman rani a garin Daberam na karamar hukumar Daura a jihar Katsina na fama da barazanar rasa amfanin gonarsu, matukar aka ci gaba da sakaci da na’urori masu amfani da hasken rana da suke amfani da su wajen yin ban ruwa daga hukumomin da abin ya shafa.

    Kimanin manoman rani dubu biyar ne a garin Daberam suka dogara akan na’urori masu amfani da hasken rana guda uku wajen yin ban ruwa ga amfanin gonakinsu tun shekarar 2021 lokacin da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya farfado da dam din.

    Gidauniya ta rabawa mata manoma ‘yan tsaki 6,000 a jihar Bauchi

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa na’ura daya ce kawai take aiki daga cikin na’urorin yayin da ragowar biyun sun lalace ba’a iya amfani da su.

    Manoman na cikin fargabar idan wata matsala ko gyara ya samu na’urar mai aikin a halin yanzu zasu iya asarar dukkan amfanin gonarsu.

    Sa’idu na Barda, wanda shi ne mai kula da na’urorin, ya bayyana cewa, “Guguwar iska ce mai karfi ta cire tare da lalata wasu bangarorin na’urorin, amma mun samu damar gano wasu bangarorin a cikin dam din muka kaiwa injiniya”.

    Ma’aikatan da aka dauka domin kula da gadin na’urorin domin kiyayewa daga barayi da masu lalata abubuwa sun yi barazanar ajiye aiki saboda ba’a taba biyansu ba tun fara aikin shekaru uku da suka gabata

    Danladi Aliyu Daberam, wanda yake aiki a matsayin maigadi a wurin ban ruwan ya ce ba’a taba biyansu ba tun da suka fara aikin.

    “Ba zamu iya ci gaba a haka ba, ba’a taba biyanmu ko kwandala ba tun da muka fara aikin kusan shekaru uku da suka gabata. Babbar matsalar mu ita ce ba zamu iya daina aikin ba, ba tare da mun mika kayan aikin ga hukuma ba.”

    Kokarin samun hukumar bunkasa ayyukan noma ta kasa domin yin magana akan lamarin ya ci tura, domin ofishin hukumar a Katsina yana rufe yayin hada wannan rahoto.

    Manoman ranin sun mika rokonsu zuwa ga gwamnan jihar Dikko Umar Radda, da ya gaggauta shiga lamarin domin kubutar da su daga asarar dukiyoyin su.

    Shehu Umar, daya daga cikin manoman ranin, ya bayyana cewa za su iya asarar kusan dukkan abinda suka noma a halin yanzu matukar ba’a gyara na’ororin ba.

    Umar ya mika rokon su ga hukumomin da abin ya shafa inda yace, “Su taimaka a gyara na’urorin masu amfani da hasken rana wadanda guguwa ta lalata, sannan a fara biyan mutanen da suke kula da su, domin ceto mu daga yiwuwar asarar amfanin gonakin mu”.

    Manoma TV

    RELATED ARTICLES

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here

    Most Popular

    Recent Comments