Cibiyar kula da albarkatun kwayoyin halitta da fasahar kere-kere ta kasa ta shawarci manoma akan zaban nau’ikan irin da ya dace da kuma ninka amfani da su domin rage sauyin yanayi.
Shugaban rikon kwarya na cibiyar, Dr Anthony Okere ne ya bayyana hakan yayin gudanar da bikin ranar manoma da bajekolin banbancin iri, da ya gudana a garin Bagauda, karamar hukumar Bebeji a jihar Kano.
> Matakin canja fasalin naira ya durkusar da manoma, inji Ministan Noma
Shugaban cibiyar, wanda ya sami wakilcin mataimakinsa Dr. Abisoye Ojo, ya bayyana cewa aikin ya samu tallafi ne daga hukumar banbance amfanin gona ta duniya da nufin dakile illolin sauyin yanayi a Najeriya.
Dr Abisoye ya ce, shirin wani bangare ne na ayyukan hadin gwiwa domin samar da ingantaccen iri wanda aka aiwatar a jihohin Oyo da Niger da kuma Kano.
A cewarsa, kimanin samfuri 150 na gargajiya da na zamani na irin dawa da wake aka shuka don hanzarta magance sauyin yanayi.
Okere ya bayyana cewa kungiyar aikin fasaha da cibiyar kula da albarkatun kwayoyin halitta da fasahar kere-kere ta kasa za su ci gaba da bayar da tallafi da jagoranci ga manoma wajen zabar iri mai inganci don bunkasa harkar noma.
Tun da fari, babban jami’in kimiyya na cibiyar NACGRAB,Dr. Muyiwa Olubiyi ya jaddada muhimmancin kiyaye amfanin gona.
A cewar Olubiyi, hakan zai baiwa masu bincike damar samun samfurin amfanin gona iri-iri a cikin bankin kwayoyin halitta don kiwo.
Ya ce ana sa ran manoman za su zabo mafi kyawu a abubuwan noma kamar dawa bisa la’akari da wasu abubuwa masu mihimmanci kamar girman iri da launin iri da kuma yawan iri da dai sauransu.
A jawabansu daban-daban, Prof. Sunusi Gaya da Dr. Ignitious Anagarawai, sun yi alkawarin ingantattun ayyukan tallafawa manoma da jagorantar su wajen zabar iri daban-daban da suka dace da harkar noma a Najeriya.
Manoma TV