Shirin ba da lamuni ga manoma na NIRSAL ya horar da malaman gona da shugabannin kungiyoyin manoma sama da dubu goma a Jigawa don tabbatar da kwarewa da kara bunkasa noman Alkama.
Manajan Daraktan hukumar ta NIRSAL, Abba Umar ne ya bayyana hakan yayin tattaunawa da y’an jarida a birnin Dutse dake jigawan.
Idan za’a iya tunawa, a watan Nuwambar shekarar 2023, gwamnatin tarayya ta kaddamar da shirin noman Alkama na kasa a karamar hukumar Auyo, inda aka kiduri aniyar noma tan 1,250,000 na Alkama a karkashin hukumar NAGS-AP a kadada 100,000 a bana, wanda dubu 40,000 daga ciki yana jihar Jigawa.
Malam Umar ya ce sun ba da horon ne domin tallafawa tsarin samar da abinci na gwamnatin tarayya na kawo kwararrun da za su iya aiki wajen habaka noman Alkama a kasarnan.
Kimanin wakilai 355 da shugabannin kungiyoyin manoma 706 daga Kiyawa da Birnin kudu da
Ringim da Hadejia da Kazaure ne suka sami damar halartar taron horaswar zagaye na farko.
Ya kuma kara da cewa an gudanar da horaswar ne a masarautu hudu daga cikin masarautu biyar na jihar.Ya bayyana cewa wadanda suka ci gajiyar wannan horon za su isar da ilimin horaswar har ma da kayayyakin aikin ga mambobin kungiyarsu.
Mr Umar ya ce an kafa NIRSAL ne domin ganin an mayar da harkar noma ta zama mai karancin hadari da kuma saukaka samar da kudaden kasuwanci ga harkar noma a Nigeria.