Wednesday, September 18, 2024
More
    HomeLabaraiFarashin kayan abinci zai sakko - Kwastam 

    Farashin kayan abinci zai sakko – Kwastam 

    Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam ta Ƙasa, Bashir Adeniyi Adewale, ya bayyana fatan cewa dakatar da karbar harajin shigo da kayayyakin abinci zai sakko da farashin kayan abincin.

    Adewale yayi bayanin cewa hukumarsa a shirye ta ke wajen aiwatar da umarnin na gwamnatin tarayya.

    Ma su zanga zangar yunwa su je su yi, mu zamu cigaba da cin abinci – Inji shugaban majalisar dattawa

    Yana bayanin hakan ne a yayin taron shugabannin hukumomin tsaro a Abuja a yau Talata.

    Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito Adewale ya ce “An yi zanga-zanga ne kan abubuwa da dama, daya daga ciki shi ne kawo karshen yunwa. Mun gano cewa kayan abinci mai tarin yawa da ake amfani da shi a Najeriya shigo dashi aka yi.

    “Daya daga cikin matakan da shugaban kasa ya dauka shi ne dakatar da karbar haraji ga kayan da ake shigo da su na abinci zuwa wani lokaci.

    Gidauniya ta rabawa mata manoma ‘yan tsaki 6,000 a jihar Bauchi

    ” Mun aminta cewa idan aka aiwatar da hakan, zai taimaka wajen sakko da farashi a kasuwanni. Hukumar hana fasa kwauri ta kasa ta himmatu wajen aiwatar da hakan”.

    RELATED ARTICLES

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here

    Most Popular

    Recent Comments