Wednesday, September 18, 2024
More
    HomeLabaraiAn Gudanar Da Sallar Rokon Ruwa Saboda Matsanancin Fari A Jihar Neja

    An Gudanar Da Sallar Rokon Ruwa Saboda Matsanancin Fari A Jihar Neja

    Shugaban Majalisar Sarakunan jihar Neja, Etsu Nupe, Alhaji Yahaya Abubakar ya jagoranci sarakuna, malaman addini da manoma a yankin masarautar Bida gudanar da sallar rokon ruwa don Allah (SWT) ya kawo karshen matsanancin farin da yankin ke fama da shi.

    Sallar wadda aka gudanar ranar Alhamis saboda matsanancin rashin ruwan wanda yafi shafar kananan hukumomi takwas na yankin masarautar matsalar da ta jawo gonakin shinkafa, masara, gero, dawa da na sauran amfanin gona suka fara konewa.

    An yi kira ga manoma da su rungumi amfani da ingantaccen iri don magance sauyin yanayi

    Manoma da dama a yankin sun ce tun makwannin da suka gabata gonakin su suka fara konewa, al’amarin da yasa Etsu Nupen ya yi kira ga al’ummar su taru a Masallacin Idi na garin Esso, Bida don rokon Allah (SWT) Ya basu ruwan sama gonaki su farfado domin samun damina mai albarka a sami abinci mai yawa a jihar da kasa baki daya.

    Da yake jawabin bayan kammala sallar rokon ruwa ruwan, Etsu Nupe yace sun gabatar da sallar ne don neman yafiyar ubangiji da rokon rahamarsa domin Musulunci ya horar da Musulmai yin hakan yayin da wata masifa ta fada musu.

    A hudubarsa, Babban Limamin Sarautar Bida, Sheikh Adamu Liman-Yakatun ya lissafo dalilan dake jawo fari da sauran masifu a cikin al’umma wadanda suka hada da rashin cika alkawari da tauye mudu daga ‘yan kasuwa da sauran al’umma.

    Liman-Yakatun yace lallai kam amfani gona na matukar bukatar ruwan sama a yankin a yayin da farashin kayan abinci yake hauhawa a kasuwanni ga kuma matsalar rashin tsaro da ta gallabi jihar.

    Binciken da wakilin MANOMATV ya gabatar ya nuna cewa matsalar rashin ruwan ta jefa manoman yankin cikin fargabar fadawa yanayin yunwa a shekara mai zuwa inda su ke nuni da cewa sun sa kudade masu yawa da suka karba bashi a gonakin.

    Daya daga cikin manoman, Salihu Ibrahim mazaunin Lemu dake karamar hukumar Gbako yace: “Ina da gonar shinkafa mai fadin shakta uku, ga gonar gero duk suna konewa saboda rashin ruwa. Bamu san abin da zai faru ba nan gaba idan farin ya cigaba, sai dai fatan Allah Ya kiyaye”.

    A nasa bangaren HarunaTswata, manomi a garin Mokwa yace yana da wahala su dawo da abin da suka kashe a gonakin su bana.

    “Na je gewaya gonata, amma bana son sake komawa domin kusan duk amfanin gonar ya kone.

    “An gaya mana cewa har yanzu akwai lokaci da zamu sake sa sabon amfani a gonakinmu amma matsalar itace mun riga mun kashe dukkan kudaden dake hannun mu a gonakin dake konewa bamu da halin fara wani abu a yanzu,’’ inji Tswata.

    Wakilinmu ya ruwaito cewa duk da Allah Ya albarkaci jihar Niger da ruwa amma guraren noman rani sun yi karanci a jihar.

    Wani al’amari dake kara mai da hannun agogo baya a fannin noma a jihar duk da cewa Allah Ya albarkace ta da kasar noma mai yawa shine matsalar rashin tsaro wanda ya jefa manoma cikin halin kaka ni kayi.

    Kananan hukumomin da suka fi fama da matsalar ‘yan bindiga da masu satar mutane a jihar sun hada da Shiroro, Munya, Rafi, Mariga, Masheku, Paikoro, Rijau, Kontagora da Borgu.

    Manoma da yawa sun yi hijara daga kananan hukumomin sannan a rufe kasuwanni masu yawa a yankunan.

    Wani manomi daga karamar hukumar Shiroro, Yahaya Dogo yace suna noma doya, wake, masara, dawa, gwaza da gero wadanda ake kaiwa kasuwanni da masanaantu kafin matsalar rashin tsaro a yankunan ta sa su hijarar dole.

    RELATED ARTICLES

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here

    Most Popular

    Recent Comments