Karamin Ministan albarkatun gona da samar da abinci na kasarnan, Aliyu Abdullahi ya ce kaso 51 na wuraren noma na fuskantar barazanr ambaliyar ruwa a bana.
Minsitan ya bayyana hakane a wani taro na horar da manoma dabarun inshora a birnin tarayya, Abuja.
>>> A share dazuka a rabawa mutane su yi noma don maganin tsaro da yunwa, inji Dr. Abdallah Usman
Ya bayyana cewa a hasashen ambaliyar ruwa ta bana da ma’aikatar ruwa ta fitar, ya bayyana cewar kananan hukumomi 148 a jihohi 31 na iya fuskantar matsananciyar ambaliya.
Ministan ya kara da cewa rahoton ya ce akwai kananan hukumomi 249 daga cikin jihohi 36 da birnin tarayya Abuja da za su fuskanci matsakaiciyar ambaliyar ruwa.
“A takaice dai kananan hukumomi 397 daga cikin 774 na kasarnan na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa. Wannan yana nufin kaso 51 na wuraren noma a kasar na fuskantar barazanar ambaliya,” inji Ministan.
A cewar Ministan kasarnan na fuskantar wannan yanayi ne sakamakon sauyin yanayi, wanda yake barazana ga shirin samar da abinci a kasarnan.
“A don hakane muke kokarin wayar da kan manoma da kuma shigo dasu cikin tsarin inshora domin zamanantar da harkokin noma a kasarnan.”