Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata ba da tallafi ga jahohin da ambaliyar ruwa ta fadawa da kudi naira billiyan uku kowaccensu don saukaka barnar da ambaliyar ta haifar.
Ministan Kudi, Mr. Wale Edun ne ya bayyana haka ya yin da yake hira da ‘yan jarida a gidan gwamnatin jihar kebbi dake Birnin Kebbi.
Kaso 51 na gonakin kasarnan na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa ~ Minista
Kamfanin dillancin labarai na kasa watau NAN ya ruwaito cewa ministan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ya kewaya wuraren da ambaliyar ruwan ta shafar a jihar.
Ministan wanda kuma shine shugaban kwamitin tattalin arziki na kasa (National Economic Council), yace “Tuni kwamitin tattalin arziki na kasa ya fara daukar matakan tallafawa gwamnatocin jahohi da kuma birnin tarayyar Abuja da kudi naira biliyan uku (3 billion) don rage asarar da ambaliyar ruwan ta haifar a wannan shekarar.
“Wadannan kudade zasu bawa jihohi, kamar jihar Kebbi, damar fara tallafawa manoma don su fuskanci noman rani cikin shiri wanda ake sa ran zai yi nasara idan aka shirya shi yadda ya kamata”.
Ya kuma ce hakan zai taimaka wajen samun nasarar samar da wadataccen abinci cikin farashi mai rahusa, zai kuma rage hauhawar farashi da daidaita tattalin arzikin kasa.
A nasa jawabin, Ministan Tattalin Arziki da Tsare-Tsare, Atiku Bagudu yace ambaliyar ruwan ta shafi kananan hukumomi da dama fiye da wuraren da ministan ya ziyarta.
Bagudu ya kuma yabawa juriya da karfin zuciyar mutanen jihar ya kuma kara da cewa za su taimaka musu a lokacin noman rani.
A nasa bangaren, Gwamnan jihar ta Kebbi Nasir Idris ya roki gwamnatin tarayya da ta tallafawa manoman saboda yawan asarar da suka yi duba da yadda ambaliyar tayi gaba da gonakin shinkafa masu yawa a jihar.
Kadan daga cikin wuraren da ministan ya ziyarta sun hada da Wacot Rice Mill da Matan Fada a garin Argungu.
Gwamnan yace a kokarin jihar na bunkasa samar da abinci, gwamnatin jihar ta raba takin zamani, iri, injin ban ruwa mai aiki da hasken rana da mai aiki da iskar gas ga manoma dubu talatin da biyar kyauta.
Daga karshe gwamnan ya yi kira ga ministocin da su taimaka su tattauna da shugaban kasa don nemo hanyar da za’a taimakawa harkokin noma a jihar domin ita kadai zata iya samar da abincin da za’a ciyar da al’ummar Najeriya baki daya.