Wednesday, September 18, 2024
More
    HomeLabaraiAmbaliya: Sama da mutane 170 sun rasu a jihohi 15

    Ambaliya: Sama da mutane 170 sun rasu a jihohi 15

    A kalla mutane 179 sun rasa rayukansu a sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihohi 15, yayin da 208,655 suka rasa mutsugunansu a jahohi 22 cewar Hukumar Bada Tallafi Gaggawa ta Kasa watau NEMA.

    Hukumar tace ambaliyar ta mamaye kadadar noma 107,652 sannan kuma ta yi sanadiyyar rushewar gidajen al’umma 80,049 a kananan hukumomi da dama.

    Ambaliya: Gwamnatin tarayya za ta bada tallafi ga jahohi

    Hukumar, wadda ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ta ce jihohin da ambaliyar tafi barna jihohin arewa ne. Asarar rayuka da barnar sun ta’azzara ne saboda ruwan sama da ake samu mai yawa akai-akai da cika da ambaliyar kogin Niger da na Benue.

    Gaba daya barnar da ambaliyar ta haifar ta faru ne a kananan hukumomi 137 daga jihohi 28.

    Hukumar tace mutane 34 ne suka rasu a jihar Jigawa, Bayelsa (25), Kano (25), Bauchi (23), Taraba (15), Zamfara (13), Sokoto (10), Yobe (10), Adamawa (7), Katsina (5), Niger (5), Borno (2), Ebonyi (2), Kaduna (2) and Nasarawa (1).

    Ambaliyar ta shafi mutane 86,000 a Bauchi, Zamfara (75,000), Sokoto (74,000), Jigawa (57,000), Niger (30,000), Kano (19,000), Imo (18,000), Adamawa (18,000), Ondo (17,000), Borno (17,000), Taraba (16,000), Kwara (12,000) sai jihar Katsina (11,000).

    Ragowar sun hada da mutane 11,000 a Yobe, Gombe (10,000), Benue (10,000), Lagos (9,000), Enugu (8,000), Kaduna (7,000), Naasarawa (6,000), Bayelsa (5,000), Ekiti (4,000), Kebbi (4,000), Oyo (2,000), Kogi (2,000), Ebonyi (2,000), Akwai Ibom (2,000) sai Babban Birnin Tarayya Abuja (1,000).

    Hukumar tace jihar Sokoto na da mutane 41,000 da suka rasa matsugunansu, Bauchi (35,000), Zamfara (32,000), Niger (28,000), Jigawa (16,000), Imo (12,000), Taraba (8,000), Borno (7,000), Bayelsa (5,000), Enugu (4,000), Adamawa (3,000), Yobe (3,000), Nasarawa (3,000), Benue (2,000), Ondo (2,000), Katsina (2,000), Ebonyi (2,000), Gombe (1,000), Kebbi (1,000), Kano (1,000), Abuja (1,000) da jihar Kogi (1,000).

    Kadadar noma 50,000 ambaliyar ta shafe a jihar Bauchi, Taraba (21,000), Jigawa (10,000), Sokoto (9,000), Niger (9,000), Kano (3,000), Zamfara (2,000), Gombe (1,000), Adamawa (1,000), Enugu (1,000) and Kebbi (1,000).

    Hukumar ta kara da cewa gidaje 18,000 ambaliyar ta rusa a jihar Bauchi, Sokoto (10,000), Jigawa (8,000), Niger (7,000), Enugu (6,000), Borno (4,000), Zamfara (4,000), Kwara (3,000), Kano (3,000), Yobe (3,000), Katsina (2,000), Ondo (2,000), Kogi (2,000), Kaduna (2,000), Oyo (1,000), Imo (1,000), Gombe (1,000), Kebbi (1,000) and FCT (1,000).

    An Gudanar Da Sallar Rokon Ruwa Saboda Matsanancin Fari A Jihar Neja

    Babbar Daraktar Hukumar, Zubaida Umar wadda ta yi wadannan bayanai yayin da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila ya kai ziyarar aiki hukumar, tace sun tattara bayanan ambaliyar daga kusan dukkannin jihohin kasar nan.

    Zubaida ta kuma kara da cewa babbar matsalar da hukumar ke fuskantar ita ce ta rashin isassun kudaden gudanar da ayyukan ta.

    A nasa jawabin, Gbajabiamila yace ya kai ziyarar ne domin sanin matsalolin da hukumar ke fuskanta don nemo hanyoyin magance su.

    Ya kara da cewa ya kamata a samar da dokar da zata sa gwamnatocin jihohi su rika bayar da tallafin kudaden gudanar da ayyukan hukumar.

    Ya kuma yi kira ga hukumar da ta mayar da hankali wajen kare faruwar ambaliyar kamar yadda take maida hankali wajen bayar da tallafi.

     

     

     

     

     

     

     

    RELATED ARTICLES

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here

    Most Popular

    Recent Comments