An tabbatar da batan manoma bakwai da rushewar gidaje 89 sanadiyyar ambaliyar ruwa a jihar Niger.
Ambaliyar, wadda ta yi awon gaba da manoman a garin Mashegu dake karamar hukumar mulki ta Magama, ta kuma lalata daruruwan kadadun noma a yankin.
Ambaliya: Sama da mutane 170 sun rasu a jihohi 15
Wasu daga cikin manoman da suka yi magana da da wakilin MANOMATV sun ce ambaliyar ta kuma yi awon gaba da dabbobi, da motoci tare lalata hanyoyin ababan hawa.
Daya daga cikin manoman, Alhaji Hassan Ibrahim yace ambaliyar ta faru ne sakamakon ruwa mai karfin gaske da aka shafe wajen awa hudu ana ana yi ranar Juma’a.
Kaso 51 na gonakin kasarnan na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa ~ Minista
Ya kuma kara da cewa garuruwan da ambaliyar ta shafa sun hada da Sabon Pegi da kuma yankunan dake makwabtakar Mashegu da Naasarawa da kuma wasu kaiyukan cikin karamar hukumar ta Magama.
Babban Daraktan Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Niger, Alhaji Abdullah Baba Arah ya tabbatar da faruwar ambaliyar.
Yace ruwa mai karfin da aka yi daga karfe biyu na dare zuwa 12 na ranar Juma’a 30 ga wata Agusta, 2024 shine sanadiyyar ambaliyar.