Tuesday, November 5, 2024
More
    HomeNoma da KiwoYadda za'a farfado da noman alkama a Najeriya 

    Yadda za’a farfado da noman alkama a Najeriya 

    Noman alkama a Najeriya ya shiga wani yanayi mai wahala sakamakon kaurace masa da manoma ke cigaba da yi musamman a jihohin da noman alkamar ya fi samun karbuwa a baya.

    Manoman na dangata ci bayan da noman alkamar ke samu sakamakon rashin samun abin da suke tsammani a kakar aikin alkamar kowacce shekara.

    NIRSAL ta horar da malaman gona sama da 10,000 a Jigawa

    A kakar noman alkamar data gabata alal misali, da yawa daga cikin manoma alkamar a Karamar Hukumar Kura dake jihar Kano sun koka game da asarar da suka yi.

    Abubakar Yusuf, wani manomin alkamar a Kura, ya gayawa Manoma TV cewa da yawa daga cikin manoman za su yi noman tumatir ne, ko masara ko kabeji maimakon alkamar a bana.

    Yusuf yace asarar da manoman suka yi ba zata rasa nasaba da wani iri mara inganci da yawancin manoman su kai amfani da shi ba.

    ‘Yan bindiga sun hallaka manoma hudu a Sokoto

    Tun kusan shekaru biyu da suka gabata, a wani hasashe da aka yi a kan fannin na noman alkamar a kasar nan wanda jari’dar Leadership Hausa ta buga, ya nuna cewa noman alkamar ya ragu daga tan dubu 600 da ake nomawa, inda a wancan lokacin ya koma tan 400, ballantana kuma yanzu da manoman ke kara ja baya.

    Manoma sun koka kan sakaci da wuraren noman rani a Daura

    A wani rahoto da gidan rediyon Rfi ya yi a watan Maris na wannan shekarar, manoma alkamar a jihar Jigawa sun koka kan karancin tallafin gwamnati ga bangaren noman alkamar.

    Wasu matsalolin da manoman na Jigawa suka dangata da jawo kalubale ga bangaren noman alkamar sun hada tsadar taki, tsadar man fetur wajen ban ruwa da tsadar man dizal don amfani taraktocin noma.

    Sakataren Kungiyar Manoma Alkama na Jigawa, Surakatu Muhammad ‘Yan Dutse, ya gayawa gidan rediyon Rfi cewa jinkirin fito da iri kan lokaci ga manoma shi ma na kawo cikas a harkar noman alkama.

    Hanyoyin farfado da noman alkama

    Bisa hirarraki da binciken da Manoma TV ta gudanar, manoma alkama a Najeriya sun bada shawarwari kan yadda za’a farfado da noman alkamar a kasar kamar haka:

    1. Bunkusa bincike don samar da ingantaccen irin alkama kamar yadda ake samarwa a fanin noman shinkafa
    2. Bawa manoma ingantaccen irin da aka samar kan lokaci kuma akan farashin dai-dai da aljihunsu
    3. Sanya tallafi da bawa manoma bashi mara ruwa kan harkokin noman alkama da sarrafa ta
    4. Samar da taki mai inganci da magungunan feshin ciyawa dana kwari  kan farashi mai sauki
    5. Rage kudin man fetur da man dizal don saukakawa manoman dake bukatar yin ban ruwan inji ga gonakinsu na alkama
    6. Inganta harkokin tsaro a wuraren da ake bukatar haka domin samar da kyakkyawan yanayi da kwanciyar hankali ga manoma
    RELATED ARTICLES

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here

    Most Popular

    Recent Comments