Shirin Bankin Duniya na Inganta Mahalli da Noma a Arewacin Najeriya watau ACReSAL ya inganta sama da kadada 1,500 don bunkusa harkar noma da kare mahalli a jihar Kogi.
Kwamishinan Mahalli na jihar, Hon. Engr. Oluwasegun ne ya bayyana haka yayin da wakilan shirin daga Bankin Duniya dana gwamnatin tarayya suka kai ziyarar aiki jihar.
An yi kira ga manoma da su rungumi amfani da ingantaccen iri don magance sauyin yanayi
Kwamishinan yace shirin ya inganta wuraren noma sama da kadada 1,500 yana mai karawa da cewa sauyin yanayi wani babban al’amari a duniya da yake bukatar hadin gwiwar hukumomi dabam-dabam.
Ya kuma kara da cewa, saboda da gudunmawar da shirin yake bayarwa a jihar, ya sa cikin dan kankanin lokaci maaikatar mahallin ta cimma abubuwa masu tarin yawa karkashin jagorancin sa.
Wakilan shirin,wadanda suka kai ziyarar aiki ta kwana shida a jihar, sun gana da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar tsaren-tsaren da shirin ke gudanarwa a Karamar Hukumar Anka a bangarorin bayar da tallafin noman rani dana inganta rayuwar al’umma.
Yadda za’a farfado da noman alkama a Najeriya
Wata wadda taci moriyar shirin a karamar hukumar, Mrs Mary Musa tace rishon girki mara fidda hayaki wanda aka samar karkashin shirin ya taimakawa rayuwar mazaunin yankin sosai wajen girki abinci cikin sauki da kare mahalli.
Wakilan shirin sun godewa babban jami’in kula da shirin a jihar, Barrister Ladi Jatto Ahmed da abokan aikin sa, sannan suka bukaci su kara maida hankali wajen tabbatar da cewa shirin na cigaba da tafiya yadda ya kamata a jihar.
Dr. Joy Iganya Agene da Engr. Chinedu Umolu ne suka shugabanci wakilan Bankin Duniya ya yin ziyarar, yayin da Abdulhamid Umar wanda ke shugabanci shirin a kasa ya wakilci gwamnatin tarayya.