Sunday, December 8, 2024
More
    HomeMuhalliBABBAN RAHOTO: Yadda Dagwalon Masana'antu Yake Gurbata Muhalli Da Harkokin Noma A...

    BABBAN RAHOTO: Yadda Dagwalon Masana’antu Yake Gurbata Muhalli Da Harkokin Noma A Jihar Kano

    Daga Anas Saminu Ja’in, Kano

    Yayin da ake cigaba da yunkurin samar da hanyoyin magance sauyin yanayi a fadin duniya, al’umma da dama ne suke fama da larura iri-iri sakamakon gurbata yanayi da manya da kananan masana’antu keyi a jihar Kano.

    Al’ummar yankin Sharada dake karamar hukumar Birni ta Kano, sun sha kokawa a lokuta daban-dabab bisa yadda kamfanonin ke haifar da gurbacewar iska, ruwan sha, matsuguni da dai sauransu, wanda hakan yake kai ga yaduwar cututtuka da ma rasa rayuka.

    Manoma sun bata sanadiyyar ambaliya a jihar Niger

    Wannan al’amari dai bai tsaya ga kan mutane ba kadai, yakan shafi gonaki dake makotaka da yankin, wanda yake lalata amfanin gona da kuma ita kasar noman kanta. Hakan dai ya zama babbar barazana da take kara karfafa illolin sauyin yanayi a fadin duniya.

    Matsalar sauyin yanayi na ci gaba da zama barazana ga manyan kasashen duniya musammam waɗanda ke da ƙarfin masana’antu masu sarrafa kayayyakin da ake amfani da su na yau da kullum.

    Manoma TV ta rawaito cewar kafa masana’antu masu sako gurbatacciyar iska da adadin mutane da ke ƙaruwa a doron ƙasa da tsarin rayuwa da ya canza, na daga cikin abubuwan da ke haifar da fargaba da samar da mummunan sakamako na ɗumamar yanayi.

    Mazauna Unguwannin Sun Koka

    A zantawar mu da wasu mazauna unguwar ta Sharada, sun bayyana yadda al’amarin yake cutar da lafiyarsu.

    Yunusa Tukur mazaunin unguwar Bubuja da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ya ce “Tabbas dagwalon masana’antu yana cutar da al’umma musamman mu da muke kusa da kamfanonin Sharaɗa.

    “A duk lokacin da aka ce an shigo irin wannan yanayin na sanyi da lokacin bazara wallahi muna shan wahala sosai saboda gurɓacewar iska, Haka muke rayuwa tsawon shekaru duk da cewa abun ya ragu ba kamar shekarun baya ba. Amma har yanzu idan aka samu sauyin iska a lokacin da masana’antu suka turo dagwalon ta magudanan ruwa muna shiga cikin tashin hankali, domin akwai shekarar da sai da mutane sukai ta kamuwa da amai da gudawa saboda wannan gubar.

    “Kullum kiran mu ga hukumomi shi ne su tuna haƙƙin miliyoyin mutane akan su ya kamata duk abun da zai zama na cutarwa ne su sanya idanu tare da magance shi.”

    Shima Isyaku Abdulkadir, mazaunin unguwar Ƴan Tagwaye ya ce “Wannan gubar da masana’antu ke amfani da ita tana cutar da mu. Tabbas ya kamata duk kamfanonin da suke fitar da wani abu da zai cutar da al’umma su canza wata hanyar ba irin wadda suke amfani da ita ba yanzu.”

    Yadda Lamarin Ya Shafi Fannin Noma

    A nahiyar Afirka ƙasar Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke sahun gaba da ƙoƙarin wayar da kai da kuma kiyaye duk abubuwan da ke iya janyo ɗumamar da yanayi ke yi.

    An yi kira ga manoma da su rungumi amfani da ingantaccen iri don magance sauyin yanayi

    Malamai da masana a makarantu da cibiyoyin nazari da kula da ɗumamar yanayi sun bayyana cewar akwai wasu kayan abinci da ba za a iya shuka su ba nan gaba. Kamar a kudancin ƙasa akwai Kwakwar Manja da Rogo da sauran nau’ikan kayan abinci dana amfanin yau da kullum. Idan aka zo yankin arewa akwai kayyakin lambu irin su Salak da dangogin sa na ɓangaren kayan miya da suke iya haɓaka tattalin arziƙin a sassan wannan kasa.

    A lokuta daban-daban a jihar Kano an taɓa samu sama da manoma 5000 waɗanda ba sa iya yin noman rani saboda sako gurɓataccen ruwa a wasu sassan na Karamar Hukumar Dawakin Kudu, Sakamakon dagwalon ruwa da ya fito daga matatar ruwan jihar Kano wanda suka yi a sarar miliyoyin nairori ta ɓangaren asarar amfanin gonar da suka irin su Shinkafa, Alkama, Rake, Tafarnuwa da Kayan Miya da sauran su.

    Malam Isma’il Ya’u manomi ne a ƙaramar hukumar Kura ya ce a shekarun baya sun tafka asara sakamakon kwararowar dagwalon masana’antu zuwa gonar su, amma a bana abun sai hamdala domin yanzu haka ya girbe amfanin gonar sa na damina har ya fara aikin noman rani wanda ya sanya Shinkafa, Tattasai da Tumatur da sauran su.

    Haka a ɓangare guda shima Mallam Zakariyya da ke noma a Dawakin Kudu ya ce “Daminar bana sai hamdala mun samu albarka, Saɓanin shekarar data gabata inda muka haɗu da iftila’i lalacewar amfanin gonar mu saboda ƙwararowa tare da bazuwar dagwalon masana’antu da ya yi a cikin gonakin mu, kuma ni har yanzu ban gama biyan irin kuɗaɗen da na ranta domin zuba jarin a noman ranin da ya gabata ba.

    “Amma yanzu an fara samun albarka da farfaɗo da abubuwan da muka rasa a baya, muna kira da gwamnati da duk wanda abun ya shafa a ɓangaren noma da su shigo ƙauyuka domin taimakon al’ummar da ke tafka asara a gonakin su.”

    Menene mafita…

    Kwamared Auwal Muhammad Abdulaziz masani a ɓangaren muhalli da ƙasa ya bayyana cewar abubuwan dake gurɓata muhalli akwai yanayin ruwa da hayaƙin masana’antu da ke lalata iska.

    Ya ce haka shima dagwalon ruwan masana’antu idan ya kwarara a ƙasar noma akwai wasu sinadarai da suke taimakawa shuka a ƙasar da ke noma.

    “Duk lokacin da sinadaran suka haɗu da shuka shi ne yake kashe ta. Akwai ƙananan halittu da sukan tallafawa shuka amma sinadarin da ke dagwalon ya fi ƙarfin su, idan muka yi duba bayan bayar da matsala ga ƙasa kuma ya haifar da rashin abincin da al’umma za su ci.

    “A duniya kashi 40℅ irin wannan dagwalon na masana’antu ya yiwa ƙasar noma illa kamar yadda hayaƙin masana’antu ke gurɓata yanayi shima babbar illa ce ga ƙasar noma saboda gurɓataccen ruwa da ake sakowa daga masana’antu ko ya bi ƙasa ko ya bi ruwa dukkanin su illar su ɗaya ce.

    Kazalika, daya daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata a mayar da hankali a kai shi ne yadda ƙasashe za su dai-dai ta al’amuran su tare da rungumar matsalolin da ke tattare da ɗumamar yanayi cikin sauki.

    A ƙasar Najeriya za a iya cewa aikin faɗakar da jama’a bai yi nisa ba, amma manyan tarurrukan da ƙasar ke halarta a kasashen waje da cikin gida na yin taimako ƙwarai wajen zaman ƙasar cikin shirin ko ta kwana musamman a wasu yankunan.

    Idan za ku iya tunawa, a shekarun baya gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira Bilyan Biyu domin gudanar da aikin magudanar dagwalon masana’antu da ke jihar Kano.

    RELATED ARTICLES

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here

    Most Popular

    Recent Comments